May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kungiyar kwadago ta janye yajin aiki

2 min read

Ƙungiyoyin kwadago na Nigeria Labour Congress (NLC) da ta Trade Union Congress (TUC) sun dakatar da yajin aikin da suka fara a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba.

Hakan ya biyo bayan wani taro da suka yi da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.

A ranar Litinin ne NLC ta yanke hukuncin tsunduma yajin aikin sakamakon dukan da aka yi wa shugabanta Joe Ajaero.

A ranar 1 gawatan Nuwamba ne Ajaero tare da rakiyar wasu mambobin NLC suka shirya wata zanga-zangar a Owerri babban birnin Jihar Imo kan zargin take haƙƙin ma’aikata da gwamnatin jihar ke yi.

Gabanin zanga-zangar ta kankama ne kuma ‘yan sanda suka cafke shugaban kungiyar kwadagon kuma aka lakaɗa masa duka, wani abu da aka zargi gwamnan jihar Hope Uzodinma da kitsawa.

Wannan ya ja ƙungiyar ma’aikata ta Nigeria Labour Congress (NLC) da ta ‘yan kasuwa Trade Union Congress (TUC) suka tsunduma yajin aiki domin nuna ƙin amincewa da wannan lamari.

Yajin aikin dai ya janyo koma baya a harkokin sufuri da na kasuwanci a sassa da dama na Najeriya.

Rahotanni na cewa wakilcin ƙungiyar ya gabatar wa da Ribadu buƙatarsa na neman a a kori kwamandan da ya jagoranci wannan aiki daga aikin ɗan sanda.

Sai dai wasu majiyoyi a Najeriya sun tabbatar da cewa Ribadu da ya shiga tsakani a wannan rikici ya ce an kama mutane biyun da ake zargi da dukan Ajaero.

Su wane ne suka shiga yajin aikin?
Zanga-zangar NLC ASALIN HOTON,FACEBOOK/NLC
Yajin aikin na ci gaba ne duk da umarnin da kotun ɗa’ar ma’aikata ta bai wa ‘yan kwadagon cewa kada su gudanar da shi.

Cikin manyan ƙungiyoyin da suka shiga yajin aikin akwai Academic Staff Union of Universities (ASUU) ta malaman jami’a a Najeriya.

Shugaban ASUU, Emmanuel Osodeke, ya faɗa cikin wata sanarwa ranar Litinin cewa “a matsayinu na mambobin NLC, muna umartar dukkan ‘yan ƙungiyarmu su shiga yajin aiki don kare haƙƙin ma’aikata da kuma shugabannin ƙungiyar”.

Jami’ar Bayero ta kano ta dakatar da jarabawar da ɗalibai ke yi ta zangon farko saboda yajin aikin.

Binciken da Sashen Pdgin na BBC ya gudanar ya nuna cewa wasu daga cikin ɗalibai sun rubuta jarabawar a safiyar Talata kafin daga baya jami’ar ta fitar da sanarwar dakatarwar.

Ba ASUU ce kaɗai take yajin aikin ba a ɓangaren ilimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *