May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Bayan ayyana Gawuna a matsayin wanda a matsayin wanda ya samu nasara me ke faruwa a Kano

2 min read

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zaman a Abuja babban birnin Najeriya ta bai wa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna kuma dan takarar APC nasara a hukuncin da ta yanke game da zaben gwamnan jihar Kano.

A hukuncin da ta yanke, Kotun ta yi watsi da ƙarar da gwamnan jihar mai ci, Abba Kabir Yusuf na jam’iyya NNPP ya ɗaukaka yana ƙalubalantar hukuncin kotun ta sauraron ƙorafin zaɓen ta jihar Kano.

A ranar 20 ga watan Satumba ne kotun sauraron ƙorafin zaɓe ta jihar Kano ta ce Gawuna ne ya lashe zaɓen wanda aka gudanar a watan Maris.

Kotun ta ce ba za a sanya ƙuri’u 165,663 da aka kaɗa wa Abba Kabir cikin lissafi ba kasancewar babu sa hannu ko tambarin kan sarki na hukumar zaɓe a jikinsu.

Hakan ne ya sanya aka zabge ƙuri’in Abba zuwa 853,939, yayin da shi kuma Gawuna ke da ƙuri’u 890,705.

Sai dai Abba Kabir ya yi watsi da hukuncin inda ya garzaya kotun ɗaukaka ƙara.

Ya bayyana sakamakon kotun sauraron ƙorafin zaɓen a matsayin “kuskure” kuma maras “adalci.”

Me ya faru a kotun korafin zaɓe?
Kano politicians
Tun farko a watan Maris, hukumar zaɓe ta ce ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf ya ci zaɓen gwamnan Kano, da ratar ƙuri’a 128,900.

Abba Kabir Yusuf, in ji INEC ya samu ƙuri’u mafi rinjaye har 1,019,602, inda Nasiru Yusuf Gawuna da ke biye da shi, ya samu ƙuri’a 890,705.

Alƙalan ƙaramar kotu, sun umarci hukumar zaɓe ta INEC ta janye shaidar cin zaɓen da ta bai wa Abba Kabir Yusuf, tare da gabatar da ita ga Nasiru Yusuf Gawuna.

An tsaurara tsaro a Kano
Rundunar ‘yan sandan a Kano ƙarƙashin kwamishinanta, Mohammed Usaini Gumel, ta gudanar da taron gaggawa da shugabannin jam’iyyun APC da NNPP a jajiberen ranar yanke hukunci.

Ta ce sun ɗauki matakai da haɗin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro a jihar don ganin ba a fuskanci rashin zaman lafiya a yayin, da kuma har bayan hukuncin kotun ba.

Kwamishina Mohammed Usaini ya kuma ce, sun tattauna, kuma sun samu tabbaci daga shugabannin jam’iyyun biyu cewa za su yi duk abin da ya wajaba don ganin ba a kawo hargitsi, saboda hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba a Kano.

Me ya rage?
Akwai damar sake ɗaukaka ƙara ta ƙarshe ga duk ɓangaren da bai gamsu ba, zuwa gaban Kotun Ƙolin Najeriya, wadda ita ce kankat.

Hukuncin na zuwa ne kwana goma cif bayan alƙalan kotun da ke zama a Abuja, sun saurari bahasin duk ɓangarorin da ke cikin shari’ar, tare da sanya hukuncinsu a mala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *