May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ko Muhuyi zai iya cika sharudan da Kotu ta nema kafin bada belinsa

2 min read

Kotun ɗa’ar ma’aikata ta bada belin shugaban hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa na jihar Kano Muhuyi Magaji Rimin Gado kan kuɗi Naira miliyan 5.

Wannan na zuwa bayan gurfanar da shi a yau Alhamis gaban kotun.

Alkalin kotun Justice Danladi Umar ya kuma sanya sharrudan belin kan Muhuyi Magaji da ake zargi da tasarrufi da kudade ba bisa ka’ida ba waɗanda yawansu ya kai Naira Miliyan 394

Kotun ta sa sharuɗɗa da sai Muhuyin Magaji ya cika sannan za’a bada belinsa, sharuɗɗan sun haɗa da, biyan kuɗi Naira miliyan 5, da kuma mutum 2 da zasu tsaya masa kuma ya zama suna zaune a birnin tarayya Abuja.

Har wa yau kotun ta bukaci waɗanda zasu tsayawa Muhuyi Magajin kafin bada belinsa sai sun gabatar da hotunansu na Fasfo guda bibbiyu.

Harwa yau sai Muhuyi Magaji ya gabatar da wasika da daga wani babban mutum da yake aiki ko kuma kasuwanci a birnin tarayya Abuja, kuma rijistaran kotun ɗa’ar ma’aikata zai tantance wasikar kafin a bada belinsa.

A kwanakin bayane dai hukumar kula da ɗa’ar ma’aikata ta maka shugaban hukumar karbar korafe -kirafen da yaki da cin hanci da rashawa na Kano a gaban kotu, kan zargin yin ba daidai ba da kuɗin da adadinsu ya kai naira miliyan 394.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *