May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Har yanzu akwai marasa lafiya 291 a asibitin al-Shifa – WHO

1 min read

Hukumar Lafiya ta Duniya, (WHO) ta ce akwai marasa lafiya 291 da ke cikin tsananin jinya a asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza, bayan a jiya ɗaruruwan Falasɗinawa sun fice daga asibitin a ƙafa.

Kashi biyu cikin uku na marasa lafiyar jarirai ne da ke cikin mawuyacin hali, kamar yadda WHO ɗin ta bayyana.

Daga cikin marasa lafiyar, WHO ta ce suna ɗauke da munanan raunukan karaya, da waɗanda aka yanke musu ƙafa ko hannu, da masu raunuka a kansu da kirji da raunukan da suka danganci cikin jiki.

Likitoci 25 ne suka rage a asibitin na al-Shifa.

A jiya ma’aikatar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce akwai kimanin marasa lafiya 120 da suka rage a asibitin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *