May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotun daukaka kara da ke zamanta a babban Birnin tarayya Abuja ta karɓe nasarar gwamnan jihar Plateau, Caleb Muftwang na jam’iyyar PDP

1 min read

Wani kwamiti mai mutane 3, a wani hukunci na bai-daya a yau Lahadi, ya ce Muftwang bai bi ka’ida ba wajen tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar PDP kamar yadda sashe na 285(2) na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

Kwamitin ya kara da cewa karar da Nentawe Goshwe na jam’iyyar APC ya kawo ya samu nasara saboda batun cancantar zabe ne na gaba da bayan zabe, a karkashin sashe na 177(c) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da sashe na 80 da 82 na Dokar Zabe, 2022..

Kotun ta umarci INEC da ta karɓe satifiket din zabe daga hannun Muftwang ta kuma baiwa Goshwe sabo.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *