May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa reshan jihar Kano ta kona kwayoyin da suka kama tun daga 8 ga watan October 2020 zuwa 17 gawatan October 2023, wadanda suke da nauyi na kimanin tan 15,193.365

1 min read

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta ƙasa reshan jihar Kano ta kona kwayoyin da suka kama tun daga 8 ga watan October 2020 zuwa 17 gawatan October 2023, wadanda suke da nauyi na kimanin tan 15,193.365.

Da yake nasa jawabin shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na kasa Wanda ya samu wakilcin na shugaban gudanarwar hukumar, Samuel Bashir, ya bayyana irin yadda wannan koyana kwayar keda muhimmanci.

Shima a nasa bangaren shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi na jihar Kano Abubakar Idris ya bayyana matsayarsu a hukumance dangane da duk Wanda suka kama yana siyar da kwaya da Kuma wasu abubuwa masu sa maye.

Taron ya samu halartar manyan Baki daga hukumomin tsaro na ciki da wajen Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *