May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Makomar Nigeria – Tinubu zai gabatar wa majalisa kasafin kuɗi na 2024

1 min read

Majalisar Zartarwa ta Najeriya ta amince da naira tiriliyan 27.5 a matsayin kasafin kuɗin ƙasar na shekarar 2024.

Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abbas ya ce nan da ‘yan kwanaki za a miƙa musu kundin kasafin domin tantancewa da amincewa.

Sai dai wasu kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito cewa shugaban zai gabatar wa majalisar kasafin a ranar Laraba mai zuwa.

Wannan ne cikakken kasafi na farko da Bola Tinubu zai gabatar wa majalisar tun bayan rantsar da shi a watan Mayun da ya wuce.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *