May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zarginmu da ba da cin hanci a shari’ar gwamnan Kano, kotu ce za ta rabu da kai – APC

2 min read

Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya bayar da wa’adin sa’a 48 ga kwamishinan shari’a na jihar, Haruna Isa Dederi, ya janye zargin cin hancin da ya yi iƙirarin shugabannin APC na Kano sun bayar don tankwara shari’a, ko kuma ya fuskanci kara a kotu.

Wata wasika da Abdullahi Abbas ya rubuta ga Dederi, kuma aka fitar da ita ga manema labarai ranar Lahadi a Abuja, ta ce babban jami’in shari’ar jihar Kano ya zargi shugabannin APC da tankwara shari’ar gwamna a kotun ƙorafin zaɓe ta jihar, da kuma hukuncin alkalan kotun daukaka ƙara da suka kori nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf na NNPP a zaɓen watan Maris.

Ta ce Dederi ya bayyana a wani gidan talbijin na kasar, yana iƙirari maras tushe da cewa hukuncin da kotun ta yanke ta hanyar Zoom, akwai katsalandan.

Abbas ya ƙara da cewa, kwamishinan shari’ar bai tsaya nan ba, ya ci gaba da tozarta alkalan kotun daukaka kara da cewa, “bisa ga bayanan da muka samu, an yi katsalandan daga masu iko”.

Wasikar ta kuma ce, “Tun bayan kalaman da ka yi a sama, na samu kiraye-kiraye da sakonnin waya masu yawa daga ‘yan uwa da abokai har ma da abokan aikina da abokan arziki, suna neman karin bayani a kan ko gaskiya ne jam’iyyata ta yi katsalandan a hukuncin da kotun ta yanke na daukaka kara.”

“Na kuma samu barazana iri-iri ciki har da yunkurin kai hari gidana da ke Kano.”

“Kalamanka na rashin hattara sun haifar da tashin hankali sosai, ta hanyar zubar min da mutuncina a tsakanin al’umma”.

Amma da yake mayar da martani, Dederi, ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa bai ga wata wasika daga shugaban jam’iyyar APC ba, ya kara da cewa rade-radi ne kawai.

“Na ji wasu na cewa, sun gani a shafukan sada zumunta, amma ba ni da abin cewa.

“Idan za a iya gabatar min da wata shaidar da ke nuna cewa ga inda na yi wata magana, kuma ga abin da na ce, to zan iya bayani ko bayar da amsa”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *