May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotun Koli ta yanke hukuncin ci gaba da amfani da tsoffi da sabbin takardun kuɗin Najeriya

2 min read

Kotun Kolin Najeriya ta bayar da umarnin a ci gaba da amfani da tsoffin takardun kudi na Naira 200, da 500 da kuma 1000 tare da sabbin da aka sauyawa fasali.

Kotun ta yanke wannan hukuncin ne yau yayin da ta yi Nazari kan wata bukata da gwamnatin tarayyar kasar ta gabatar ma ta.

Kotun kolin dai ta yanke hukuncin cewa duka sabbin da tsoffin takardun kudin za su ci gaba da zama kudi har gwamnatin tarayyar kasar ta shirya ma canja tsoffin bayan tattaunawa da dukkan masu ruwa a lamarin.

Haka na nufin wannan hukuncin ya shafe wanda kotun ta yanke a farko shekarar nan cewa za a ci gaba da amfani da tsoffin kudin har zuwa ranar 31 ga watan gobe na Disamba.

Kotun dai ta yanke hukunci ne kan wata bukata da gwamnatin kasar Ta shigar gabanta ta hannun babban lauyan gwamnati Leteef Fagbemi a makon jiya, inda ta nemi kotun da ta soke hukuncin nata na baya cewa tsoffin kudin za su daina aiki daga ranar 31 ga wata Disamba.

A cikin hujjojin da ta gabatar, gwamnatin ta yi wa kotun bayanin cewa idan kotun ta ki amincewa da wannan bukatar, to kasar na cikin kasadar sake fadawa cikin wata sabuwar matsalar karanci kudi da ci bayan tattalin arziki irin wadanda aka gani a watanni ukun farko na wannan shekarar lokacin da babban bankin ya yi canjin sabbin kudi.

Babban lauyan gwamnatin ya shaidawa kotun cewa ya kamata a tsawaita wa’adin tsoffin kudi ta yi la’akari da yadda tuni wasu ‘yan kasar suka fara taskace duka sabbi da tsoffin kudin ganin wa’adin nata na 31 ga watan Disamba na karatowa.

Kimanin Makonni biyu da suka wuce ne dai Babban Bankin Kasar ya sanar da cewa tsoffin takardun Naira 200 da 500 da kuma 1000 za su ci gaba da zama kudin har illa masha Allahu; abin hukuncin kotun kolin ya kara tabbatarwa a yau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *