May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Zanga-zanga ta barke a Kano kan zargin harbin matasa

1 min read

Dandazon matasa sun gudanar da wata zanga-zanga a unguwar Kurna da ke tsakiyar birnin Kano, inda suka toshe babban titin zuwa Katsina tun da safiyar yau domin nuna fushinsu a kan harbin wasu matasa.

Suna zargin ƴan sanda da harbin matasan ne, wanda ya yi sanadin mutuwar daya daga ciki, karin wasu biyu kuma sun samu raunuka har ma an kwantar da su don yin jinya a asibiti.

A baya-bayan nan, ana fama da tunzuri saboda shari’ar zaben gwamnan jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce tuni an kama dan sandan da ake zargi da yin harbin na ranar Talata, wanda ya kai ga matasan gudanar da zanga-zanga a wayewar gari.

A ciki wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce dan sandan mai mulkamin sufeto ya yi harbi kan kungiyoyin matasan da ke rikici da juna ne inda ya raunata biyu, daya kuma ya riga mu gidan gaskiya.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, Mohammed Usaini Gumel, ya ba da umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

A cewar sanarwar tuni aka kama sufeton, kuma a halin yanzu yana tsare a hannun ‘yan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *