May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Yan sanda sun kama wani hadimin gwamnan Kano bisa zargin karkatar da abincin tallafi

1 min read

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama Tasiu Al’amin-Roba, babban mataimaki na musamman (SSA), ga gwamnan jihar kano a kabinet ofis da kuma wani Abdulkadir Muhammad bisa zargin su da karkatar da kayan abincin tallafi a jihar Kano.

Kwamishinan ‘yan sandan, Hussaini Gumel, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya hakan a wata hira ta wayar tarho a ranar Lahadi cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada dauke da jakunkuna sama da 200.

Ya kara da cewa wadanda ake zargin sun yi awon gaba da shinkafa da masara a ma’ajinar da ke Sharada.

“Tun daga lokacin ne muka fara bincike mai zurfi don gano buhunan masara ko shinkafa nawa aka diba aka sayar da su,” inji shi.

Gumel ya ce za a gurfanar da mutanen biyu a gaban kotu bayan kammala bincike.

KD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *