May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Muna Allah wadai da kisan Al’ummar Musulmai masu Maulidi wanda sojojin Nigeria sukai a Kaduna -Bakin Bulo Network For Better

1 min read

Kungiyar Bakin bulo Network For Better tomorrow ta yi Allah wadai da kashe masu Maulidi a jihar Kaduna wanda sojojin Nigeria sukai

Shugaban Kungiyar Bilal Nasidi Muazu ne ya bayyana haka a yayin taron manema Labarai da Kungiyar ta gudanar a yammancin Talata.

Ta bukaci Makaman Addini da su cire BANBANCIN dake tsakaninsu domin Karbo hakkin mutanan da basu jiba kuma basu gani ba.

Ta cikin sanarwar da Kungiyar ta fitar ta bukaci Yan Siyasa da Dattawan Arewa dasu ta shi tsaye wajen kare martabar Al’ummar arewa ganin cewa ba wannan ne karo na farko da ake samun irin wannan lamari yana faruwa ba.

Kungiyar ta Kuma yi kira ga Gwamnati tarayya da ta tabbatar ta dauki mataki akan sojin da suka aikata wannan ta’addanci tare da biyan diyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa dasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *