May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Matasa a Kano sun bukaci Tinubu ya shiga lamarin Kano domin adalci

1 min read

Gamayyar ƙungiyar matasa masu rajin samar da cigaba a jihar Kano, sun yi kira ga shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, akan ya sanya baki cikin batun shari’ar zaɓen Kujerar gwamnan Kano, musamman wajen kira ga Alƙalai da su tabbatar sun bawa al’ummar jihar Kano haƙƙinsu a kotun ƙoli.

Shugaban ƙungiyar, Ibrahim Rabiu, ne ya bayyana haka ranar Laraba yayin da tattaunawarsa da manema labarai, inda ya ce bai kamata mutane su fito suyi zaɓe kuma a kwace musu ba, yin hakan kamar karya Demokradiyya ne, kuma za’a karya gwiwar mutane masu zaɓe.

A karshe, ƙungiyar tayi kira ga tsofaffin shugabannin ƙasa, shugabannin Addini dana gargajiya da suyi kira wajen tabbatar da haƙƙin al’ummar jihar Kano da suka zaɓi jam’iyyar NNPP ya tsira a kotun ƙoli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *