June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

CENTER FOR ETHICS AND SELF VALUE ORIENTATION ta zabi Emirates College a matsayin Kwalejin ta daya a Kano a yayin da tazo ta takwas cikin kwaleji talatin masu zaman kansu a faɗin Nigeria

2 min read

Exif_JPEG_420

Wannan cibiya watau CENTER FOR ETHICS AND SELF VALUE ORIENTATION ta ce tayi binciken kwafkwafi na tsahon Lokaci a kan yadda Emirates College ke gudanar da ayyukanta musamman koyo da koyarwa bisa gaskiya da Amana.

Exif_JPEG_420

Exif_JPEG_420
Exif_JPEG_420
Exif_JPEG_420

Exif_JPEG_420

Daraktan cibiyar Salim Musa Yakubu ya shaidawa manema labarai irin ayyukan da suka bibiya wanda Emirates din gudanarwa Kuma mun gamsu bayan Sanya Ido ba tsahon Lokaci batare da koya yasan muna yi ba.

Ya kara da cewa da mun samesu da almundana ko wani rashin gaskiya irin yadda wasu makarantu ke gudanarwa to babu shakka sai mun fito mun fadawa duniya cewa karya suke duk abubuwan da suke bayyanawa.

Shima da yake jawabi Jim kadan bayan kammala taron Bada lambar yabo Makarantar Jami’in Yada labaran Makarantar Malam Abdul Kabir Sulaiman ya ce wannan lambar yabo ya kara masu kwarin gwiwar cigaba da gudanar da ayyuka batare da gajiyawa ba.

Alhaji Dakta Shu’aibu Sulaiman Garkuwan Marayu da marasa galihu Wanda shi Shugaban Makarantar Emirates College yayi godiya ga Allah bisa wannan matsayi da suka samu a yau sai ya ce wannan shi ne Babban ƙalubale a garesu inda ya dole su kara dagewa abisa ayyukansu.

Ya Kara da cewa duk Daliban dake bukatar ilimi Makarantar ta samar da kayan koyo da koyarwa da malamai ingantattu domin cigaban bangaren harkar lafiya.

Ya Kuma bayyana godiya ga Malaman karantar dake bada gudunmawa a kullum Wanda da gudunmawarsu ne Makarantar da dalibai ke samun nasara a kullum.

A yayin taron dai a raba lambobin yabo ga Malaman dake sassan Makarantar bisa kwazo da suke nunawa a ayyukan su na yau da kullum.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *