July 12, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kisan Masu Maulidi: Gwamnati ba da gaske take ba wajen yiwa musulmi adalci – Falakin Shinkafi

2 min read

Falakin Shinkafi, Amb. Yunusa Yusuf Hamza yace bai gamsu da matakan da gwamnatin tarayya ta ce zata dauka don nuna damuwarta da abun da sojoji suka yi na sakin bom akan mutanen dake Maulidi a garin Tudun biri dake karamar hukumar igabi a jihar Kaduna.

” Tunda abun nan ya faru duk abun da gwamnatin tayi da sunan alkawari ta yi shi wanda mu Muna ganin gaskiya ba lallai su iya cika alkawuran ba, tunda da da gaske suke da yanzu a lalubo wadanda sukai abun an Kuma fara hukunta su, ba ayi ta yi mana alkawura ba”.

Amb. Yunusa Yusuf Hamza ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar Kadaura24 ta a Kano.

Yace ya kamata ya zuwa yanzu an kafa kwamitin bincike ko ma an kamo wadanda suke da hannu akan lamarin domin daukar mataki , Maimakon alkawura da ake ta tayi.

” Batun diyya ma ya kamata ya zuwa yanzu ake mun ji ma’aikatar tsaron Nigeria ko ita kanta gwamnatin tarayya ta fitar da kudaden da za’a biya diyyar rayukan wadancan bayin Allah da aka kashe ba tare da laifin komai ba”. A cewar Falakin Shinkafi

“Mu a matsayin mu na yan arewa Musulmi ba zamu saurara ba, har sai mun ga an tabbatar da adalci akan wadancan bayin Allah, ta hanyar hukunta masu hannu a lamarin da kuma biyan diyyar rayukan mutanen da aka kashe babu gaira babu dalili”.

Nasara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *