June 13, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta gano sabon salon da direbobi ke yi wajen shigo da Giya jihar Kano

1 min read

Shugaban Hukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a yau.

Lokacin da yake yaba kokarin jami’an Hukumar, wadanda suka sami nasarar gano dabarun da Direbobi ke yi wajen shigo da giyar jihar Kano

Hukumar ta ce ta sami nasarar cafke mota kirar Canta Mai lumbar FGE 407XB Wanda ta dakko giya fiye da kwalaba Dubu Hudu (K4600)

Jami’an da suka sami nasarar cafke motar sun bayyana cewa lokacin da suka tsayar da motar Direban ya bayyana musu cewa Itacan girki ya dakko, bayan da aka matsa bincike sai aka fahimci ba itacen ba ne Barasa ce a ciki

Shugaba Hukumar Engr. Faisal Mahmud Kabir ya ce bayan an kammala bincike za a mika Giyar ga Hukumar Hizba domin fadada bincike tare da daukar mataki na gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *