May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar’yan sandan Najeriya tace yan ƙasar na da damar ɗauar bidiyo da hotunan ‘yan sanda a lokacin da suek bakin aiki

1 min read

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ƙasar, Muyiwa Adejobi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa a ranar Alhamis.

Rahotanni sun bayyana c Cewa adejobi na mayar da martani ne kan saƙon da wani mai amfani da shafin ya wallafa da ya ce ‘yan sanda sun tatse shi naira 10,000 saboda bidiyon da ya ɗauke su a lokaci da suke binciken ababen hawa.

Kakakin rundunar ya ce ba laifi ba ne ɗaukar hoto da bidiyon ‘yan sanda a lokacin da suke bakin aiki.

Ya ƙara da cewa rundunar ta sha gaya wa mutanen cewa babu laifi ɗaukar bidiyo da hotunan ‘yan sandan da ke bakin aikin.

Mista Adejobi ya ce duk wanda ‘yan sanda suka ci zarafinsa saboda ɗaukarsu bidiyo ko hoto su kai rahoto ga hukumar ‘yan sanda.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *