May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Musulunci ya samu karuwar a kasuwar sayar da wayoyi ta Beirut Dake Kano

1 min read

Wata matashiya Dake aiki a kamfanin Fagge Communication wadda suke bayar da wayoyi bashi ta shiga addinin Musulunci a wannan Rana ta juma’a

Matashiyar wadda abaya sunanta ( Dokas ) amam yanzu ta zabi sunan Zainab amatayin sunan da take so a rika kiranta dashi

Matashiyar wadda Ta shiga addinin karkashin kamfanin Fagge Communication kuma sheikh Dr Bashir aliyu Umar shine ya musuluntar da ita Jim kadan da kammala sallar Juma’a a masallacin alfurkan.

Ta Bayyana cewa yadda taga musulmai suna yin sallah Bai Daya da kuma Nutsuwa yayin da suke yin sallah, da kuma yadda mata musulmai suke Sanya Hijab yana daga abinda yaja hankalinta wajen komawa addinin Musulunci

Ta roki al’ummar musulmi da su dauketa amatayin Yar uwarsu kasancewar kyawawan dabi’un musulunci yasa ta koma addinin Musulunci daga addinin Kirstanci.

Mikiya Hausa Times Ta ziyarci kamfanin Fagge Communication wadda anan ne matashiyar take aiki kuma Shugaban kamfanin Alhaji sule ya Bayyana Jin dadinsa da samun karuwa da addinin Musulunci yayi.

Yace Babu Wanda ya Tilasta mata kawai dai ta gamsu da yadda musulmai ke gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *