May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Jihar Kano Ta Fara Bincike Kan Gobarar Da Ta Tashi A Sakatariyar Karamar Gwale

2 min read

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta binciki musabbabin barkewar gobarar da ta tashi a sakatariyar karamar hukumar Gwale.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa lamarin wanda ya faru a ranar 13 ga watan Disamba ya shafi ofisoshi 18 tare da lalata kadarori na miliyoyin Naira.

Sai dai Jaridar Global Tracker ta ruwaito cewa Mataimakin gwamnan jihar Aminu Gwarzo ne ya sanar da hakan a wata ziyarar da ya kai sakatariyar majalisar da abin ya shafa domin duba irin barnar da gobarar ta yi.

Ya bayyana cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na aiki tukuru don ganin an yi adalci a hukuncin kotun koli mai zuwa.

Mista Gwarzo, wanda shi ne kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, ya buƙaci al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda.

Ya kuma tabbatar da cewa duk da tashin hankali da ake fama da shi a jihar saboda lokacin da ake jira a yanke hukunci, gwamnatin mai ci ba za ta shagaltu da samar da ayyuka na yabawa da za su daukaka rayuwar al’umma ba.

Ina tabbatar muku da cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba har sai an gano wadanda suka aikata laifin kuma a hukunta su

Yanzu dai Babu wani Abu da al’ummar jihar kano ke yawan tattaunawa akansa Kamar batun shari’ar zaben gwamnan jihar.

Wakilin jaridar Inda Ranka Yasir Sani Abdullahi ya gano yadda kusan da yawa daga cikin wuraren zaman al’ummar da kasuwanni harma da ofisoshin gwamnatin da masu zaman Kansu, Babu wani batu da yafi daukar hankali Kamar batun shari’ar

Magoya bayan dukkan babgarorin manyan jam’iyyun APC Dana NNPP na bugar kirgin samun nasara a kotun koli.

Jam’iyyar APC na da kwarin guiwar cewa Zata Kara samun nasara a kotun koli kasancewar kotun farko da ta biyu duka ta Bata nasara.

Sai dai jam’iyyar NNPP Bayan korafe-korafe da tayi akan hukunce hukunce na kotun baya, yanzu ta bayyana kwarin guiwar da take dashi na samun nasara a kotun koli.

Al’ummar jihar kano da dukkan bangarorin manyan jam’iyyun APC Da NNPP na dakon hukuncin na karshe na kotun koli wadda ake saran Zata yanke cikin karshen watan Nan, shi zai kawo karshen jayayya da kowane bangare keyi a jihar kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *