May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Na Rantse da Allah a iya labarin Yarannan mawadata da sauran Al’umma Allah zai barmu ba

2 min read

MUN SAMU ZUWA GURIN YARANNAN DA MAHAIFINSU KE DAURE A PRISON

Alhamdulillah mun samu zuwa gurin yarannan wanda aka daure mahaifinsu a prizon tsahon shekaru matar shi kuma ta rasu tabar yaranta har da jaririya, wanda yaran ke rayuwa su kadai.

Kamar yadda muka sanar da ku mai girma Gwabnan Kano H.E Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a kaiwa yaran daukin gaggawa mun sanu mun kai musu kayan abinci da katifar da za su dinga kwanciya saboda a kasa suke kwanciya shi ya sa suka kamu da ciwon sanyi wanda Mai Girma Gwabna ya bayar da umarnin a duba lafiyarsu inda mai girma shugaban asibitin Hasiya Bayaro ya tura aka je har gida aka dauko su aka kaisu asibitin aka musu gwaje-gwaje an gano suna fama da cuwuka kala-kala, an ba su magunguna, sannan mai girma Gwabna ya bayar da umarnin gurin mai girma Kwamishinan Shari’a akan ayi duba ga halin da mahaifinsu ke ciki a dauki matakin gaggawa akan lamarinsa.
Yanzu haka kuma zaa saka su a makarantar Islamiyya sannan idan an koma makarantar Boko a watan Janairu zaa mayar da su makarantar Boko.
Allah ya sakawa mai girma Gwabnan Kano da alkairi, Allah ya bashi ikon ci gaba da jin kukan Al’ummar Kano, Amin ya Allah

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *