May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa zai sanya baki don hana Shoprite barin Jihar Kano

2 min read

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, zai sanya baki don dakatar da yunkurin da katafaren shagon hada-hadar kasuwanci na Shoprite ya ɗauka na rufe reshensa daya tilo a jihar Kano.

Katafaren kantin sayar da kayayyakin dake Ado Bayero Mall a Kano, a makon da ya gabata sun sanar da matakin ficewa daga cibiyar kasuwanci a watan Janairun da zai kama, inda suka bayyana cewa hakan ya biyo bayan yanayi na kalubalen tattalin arziki da ake fuskanta.

An samu ra’ayoyi daban-daban dangane da matakin da Shoprite ta dauka wadda ke aiki a jihar Kano tun watan Maris na 2014.

Wata sanarwa da mai baiwa Sanata Barau shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a Ismail Mudashir ya fitar ta ce mataimakin shugaban majalisar dattawan zai gana da mahukuntan kamfanin a cikin makon nan a Abuja kan lamarin.

‘’ Ofishin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan ya tanadi tsari mai kyau don dakatar da Shoprite daga dakatar da kasuwanci a Jihar Kano. Mai girma mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I Jibrin, CON, zai gana da mahukuntan kamfanin a wannan makon inda za a tattauna batun da fatan shawo kan lamarin.

‘’Duk da batun kasuwanci ne tsantsa, amma za mu ga abin da za mu iya yi don karfafa musu gwiwa su janye yunƙurin da suka yanke kuma su cigaba da kasuwanci a Kano. Kamar yadda kowa ya sani, akwai dimbin damammakin kasuwanci a Kano, cibiyar kasuwanci ce ta Arewacin Najeriya. A lokacin da muke zawarcin masu saka hannun jari, ba za mu nade hannayenmu mu kyale su su tafi ba,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *