May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar kula da ingancin Kayayyaki ta Kasa Standards Organisation ta bukaci Al’umma dasu ringa kai rahoton Bullar Kayayyaki marasa inganci

1 min read

Babban Darakta a hukumar dake jihar Kano, Malam Muhammad Jibril ne, ya bayyana haka a yayin da yake amsa Tambayoyi ga manema labarai a hukumar dake nan Kano.

Daraktan ya kara da cewa idan Al’umma sun sun Sanya Ido ido tare da kai bayanan sirri akan duk wasu kayayyaki da suka tarar basu da shaidar inganci daga hukumar, to tabbas hukumar bazatai kasa a gwiwa ba wajen daukar matakin da doka ta tana akan duk wanda aka kama da laifin.

Ya Kuma ce, tashin Kayayyaki da ake samu a kasar nan ya taimakawa batagari shigo da wasu daga cikin kayan da Al’umma ke amfani dasu marasa inganci

Malam Muhammad ya Kara da cewa akwai hukunce-hukunce da hukumar ta tanada akan dukkan wadanda aka kama da shigo da kayan da basu da inganci.

Hukumar ta SON ta ce bazata saurarawa duk wani kamfani ko masu shaguna ko Kuma wani guri da ake hada-hadar Kaya marasa inganci ba,a dan haka yayi kira ga duk masu irin wanda dabi’a dasu kuka da kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *