July 18, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Jihar Kano ta ce wajibi ne kula da Mata da kananan Yara a Asbitocin Jihar

2 min read

Exif_JPEG_420

Kwamishinan lafiya na Jihar Kano Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ne ya bayyana haka, wanda Dakta Nasir Mahmud DG Primary Health Management ya wakilta, yayin taron manema Labarai da masu ruwa da tsaki a bangaren lafiya, wanda ya gudana a Asbitocin Muhammad Abdullahi Wase dake nan Kano.

Kwashinan ya ce, an ware sati guda domin kula da Mata musamman masu juna biyu da kananan Yara a faɗin kananan hukumomin Jihar Kano 44.

Exif_JPEG_420

Ya kara da cewa Gwamnatin jihar Kano ta Kuma cigaba da baiwa kananan Yara alluar rigakafi sakamakon wasu alamomi da suka fara bulla a wasu daga cikin makotan jihar,inda ya ce Shekara tara kenan rabon jahar kano da masu bafa da polio.

Dakta Nasir ya kuma kasan cewar wasu makotan Jihar an samu bullar ta, shi ne ya Sanya kara bukatar Gwamnati tashi tsaye wajen Kare kananan Yara.

Ya ce, Asbitoci sama dubu da 120 ne zasu duba matan da kanan yara wanda za’a basu magungunan da suka kamata, da kuma basu shawarwari domin cigaba da inganta lafiyarsu.

Exif_JPEG_420

Ya Kuma cewa wanda aka ga suna da bukatar kulawa ta musamman, suma za’a tura su Asbiti na gaba domin cigaba da kula dasu.

Dakta Nasir Mahmud ya Kuma ce, Gwamnan Kano Engr Abba Kabir Yusuf, ya umarci ma’aikatar lafiya da ta tabbatar Al’ummar jihar Kano sun samu kulawa ta musamman a dukkan manya da Kuma kananan Asbitocin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *