May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hamas na zargin Isra’ila da yi wa Falasɗinawa 130 kisan gilla a Gaza

1 min read

Ƙungiyar Hamas ta zargi sojojin Isra’ila da aiwatar da kisan gilla a zirin Gaza.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce ta samu bayanan shaidun gani-da-ido na cewa sojojin Isra’ila sun kashe Falasɗinawa sama da 137 a arewacin yankin da kuma Birnin Gaza, suka sanya su cikin manyan ramuka tare da harbe su.

Wakilin BBC ya ce sun kuma zargi sojojin na Isra’ila da kashe ƴan jarida sama da 100, da mata masu ciki a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa asibiti a arewacin Gaza.

Rundunar sojin ta Isra’ila ta ce ba ta da masaniya kan lamarin.

Hamas ta ce hukuncin kisan wani ɓangare ne na kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa al’ummar Falasdinawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *