May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

EFCC ta bankado badakalar N37bn a ma’aikatar jinkai ta tsohuwar ministar Buhari

2 min read

Hukumar Yaki da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta bankado wasu makudan kudade samada Milyan-Sau-Milyan dubu 37 (N37,170,855,753.44) da ake zargin an karkatar da su a ma’aikatar jin kai a karkashin tsohuwar minista Sadiya Umar-Farouk.

A cewar rahoton jaridar The PUNCH a ranar Lahadi, an fitar da kudaden ne daga asusun gwamnatin tarayya, kuma an aikasu zuwa asusun bankuna daban-daban guda 38 dake cikin wasu manyan bankunan kasuwanci guda biyar na wani dan kwangila, James Okwete.

Bayan samun kudaden, Okwete ya mikawa ‘yan kasuwan canji samada N6,746,034,000.00, ya ciro tsabar kudi ahannu N540,000,000.00, ya siyo motoci na alfarma da kudi kusan N288,348,600.00, sannan ya sayi gidaje na alfarma a Abuja, da jihar Enugu, da N12,510.000.00.

Kamfanoni 53 ne ake zargin Okwete ne, wanda kuma aka ce sun yi amfani da 47 daga cikin kamfanonin wajen ujoron kwangilolin da suka kai N27,423,824,339.86. Haka kuma an danganta shi da asusun banki 143 a cikin bankunan kasuwanci 12 inda asusu 134 ke da asusun kamfanoni da ke da alaƙa da kamfanoni daban-daban.

Binciken da Hukumar Al’amuran Kamfanoni ta gudanar ya nuna cewa Okwete darakta ne a kamfanoni 11 daga cikin 53, yayin da sauran asusun kamfanoni 42 ke da alaka da Lamban Tabbatar da Bankin sa (NIN) a matsayin mai sanya hannu a asusun.

Takardar ta EFCC ta bayyana cewa, “Tsakanin 2018 da 2023, Okwete ya karbi kudi N37,170,855,753.44 daga asusun gwamnatin tarayya da ke da alaka da ma’aikatar jin kai, magance bala’i da ci gaban al’umma.

A shekarar 2020, hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuffuka ta ce ta bankado N2.67bn da ake nufi da shirin ciyar da ‘yan makarantu a cikin wani asusun banki mai zaman kansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *