May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Martani- Ƙazafi ake min, ban buɗe asusun banki 593 a ƙasashen waje ba – Godwin Emefiele

2 min read

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya musanta zarge-zargen satar dukiyar ƙasa da ake yi masa a wani rahoton Mai Bincike na Musamman kan harkokin bankin CBN da aka fitar a baya-bayan nan.

Ya bayyana matsayin nasa ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Re: Emefiele, others stole billions, illegally kept Nigeria’s funds in foreign banks’ da ya fitar ranar Lahadi.

Idan za ku iya tunawa a cikin makon jiya ne, Mai Bincike na Musamman kan harkokin Babban Bankin Najeriya, Jim Obaze, ya bankaɗo cewa tsohon gwamnan bankin ya jibge fam miliyan 543, 482,213 ba tare da izini ba a bankunan Birtaniya kawai.

Wani ɓangare na rahoton Jim Obaze a cewar jaridar Daily Post ta intanet, “Tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya jibge kuɗaɗen Najeriya ba tare da izini ba a asusun ajiya 593 na bankunan ƙasashen waje a Amurka da China da Birtaniya, lokacin da yake mulki.

Sai dai Godwin Emefiele a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce, bayan sakin sa a matakin beli daga gidan yarin Kuje, hankalinsa ya kai kan wasu labarai masu alaƙa da rahoton Jim Obaze.

“Na karanta labaran, kuma da ƙarfin murya ina cewa abin da suka ƙunsa, ƙarairayi ne da karkatar da hankali da kuma maƙarƙashiya don a ɓata min suna, a ci mini zarafi sannan da biyan muradin mai binciken.”

Ya kuma ce ba shi da hannu a buɗe asusun ajiya 593 a sassan duniya, kuma bai ma san an buɗe su ba.

Sai dai ya ce akwai sashe-sashe na babban bankin da ke da iko su aiwatar da irin waɗannan harkoki kamar yadda doka ta amince musu bisa tanade-tanaden aikin CBN.

Don haka, a cewar Emefiele “Ni ma kamar sauran ‘yan Najeriya masu kyakkyawar niyya da suka yi magana kan wannan batu, ina neman a gudanar da cikakken bincike kuma a fayyace komai a faifai game da waɗannan zarge-zarge na almundahana”.

Ya kuma ce ya umarci lauyoyinsa, su hanzarta ɗaukan matakan shari’a don wanke sunansa daga kalaman ɓata-suna da ke ƙunshe a cikin rahoton da kuma labaran da suka wallafa shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *