May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa

1 min read

Nijar ta dakatar da haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa
Nijar ta dakatar da dukkan ayyukan haɗin gwiwa da ƙungiyar ƙasashe rainon Faransa da ake kira (OIF) a taƙaice, a cewar shugabannin mulkin sojin ƙasar, yayin da take ƙara janye jiki daga tsohuwar uwargijiyar mulkin mallakarta.

Ƙungiyar mai wakilai 88 “a ko da yaushe Faransa na amfani da ita a matsayin wani makami wajen kare muradan Faransa”, a cewar wani mai magana da yawun shugabannin mulkin sojin kamar yadda ya bayyana a wani jawabi ta kafar talbijin ɗin ƙasar ranar Lahadi.

Tun cikin makon jiya ne, ƙungiyar ta OIF ta dakatar da mafi yawan ayyukan haɗin gwiwa da Nijar saboda juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Yulin 2023, sai dai ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da harkokin da “kai tsaye za su amfani fararen hula da kuma waɗanda za su tallafa wajen mayar da Nijar kan mulkin dimokraɗiyya”.

Taken da ƙungiyar ke bayyanawa shi ne bunƙasa harshen Faransanci da tallafawa harkokin zaman lafiya da dimokraɗiyya da ƙarfafa gwiwar haɓaka ilmi da raya ƙasa a ƙasashe rainon Faransa a faɗin duniya, waɗanda da yawansu tsoffin ƙasashen Faransa ta yi wa mulkin mallaka ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *