May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Akwai bukatar likitoci masu kula da al’umma a matakin farko su cire san zuciya da neman kudi a yayin da suke gudanar da ayyukan su

2 min read

Dan adalan Gaya Alhaji Abbas Jibril Kazurawa ya bukaci likitoci masu kula da Al’umma a matakin farko reshen jihar Kano dasu cire san zuciya da neman kudi a yayin da suke gudanar da ayyukan su.

Alhaji Abbas ya bayyana haka ne a yayin toron Shekara -shekara tare da wayar da kan sababbin shugabanin Kungiyar ma’aikatan lafiya masu kula da Al’umma matakin farko kai dan gudanar da ayyukan su cikin nasara.

Mai Girma Hakimin Kara da cewa matukar aka tsaya aka kula da lafiyar Al’umma a matakin farko to tabbas za’a samu raguwar marasa lafiya a Asbitocin Jihar Kano.

Ya Kuma ce, dole likitocin su kyautata alakar su da jama’a, da Kuma marasa lafiya a ko da yaushe domin samun nasarar gudanar da ayyukansu.

A jawabin sa Sabon Shugaban Kungiyar Kwamared Khalid Hussain, ya ce matsayin sababbin shugabanin Kungiyar ma’aikatan lafiya masu kula da Al’umma matakin farko, shi ne gyara tsarin
koyo da koyarwa a tsakanin ma’aikatan.

Ya Kuma sha alwashin yin dukkan maiyuhuwa wajan ganin Kungiyar ta samu Ofishinta wanda hakan zai kara kawo wa Kungiyar cigaba, musamman ma wajen gudanar da ayyukan ta na yau da kullum.

Shi ma da yake jawabi Sakataren Kungiyar Kwamared, Kwamared Aliyu Ado Kabo ya ce taron ya fadakar da sababbin yayan Kungiyar da aka zaba yadda ya kamata ssu gudanar da jagorancin Kungiyar tun daga matakin kananan hukumomin Jihar Kano 44 Kamar yadda doka ta shinfida.

Ya Kara da cewa Babban abinda ya kamata su kara dagewa a Kai shi ne, sanya kula da lafiyar Al’umma, wanda shi abinda aka san Kungiyar akai a koda yaushe.

A yayin taron dai an Gabatar da mukalu da suka shafi cigaban Al’umma dana ‘Ya’yan Kungiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *