May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gobarar tankar mai ta halaka mutum 40 tare da jikkata wasu da dama

1 min read

Kafar yada labaran Liberia ta sanar da mutuwar mutane 40, wasu sama da 30 sun jikkata a lokacin da wata tankar mai ta kama da wuta, kamar yadda wani jami’in lafiya ya shaida.

Francis Kateh, ya ce tankar man ta yi alkantara daga bisani ta fada wani rami a kan titin Totota da ke yankin Lower Bong, mai nisan kilomita 130 daga babban birnin kasar Monrovia, kuma mutane da dama sun jikkata.

Kateh ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP zai yi wuya a gano musabbabin hatsarin, sakamakon yawancin wadanda suka mutu sun kone kurmus sai tokarsu.

”Tawagar jami’anmu na kan hanyar zuwa inda lamarin ya faru, za su shiga gida-gida domin duba wadanda suka bata.”

Rahotanni sun bayyana an garzaya da gwamman mutane asibiti sakamakon mummunar kunar da suka samu, kuma Mr Kateh ya ce adadin wadanda suka mutu ka iya zarta 40 nan gaba.

Ganau sun ce wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su, sun kone ko mutu ne sakamakon kokarin kwasar ganimar man fetur da ke zuba daga tankar wanda su ne suka kara hudawa domin kwasar ganimar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *