May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnan Kano ya kaddamar aikin ginin gadar Tal’udu

1 min read

Gwamnan Kano ya kaddamar da aikin gadojin sama na Dan Agundi da ta Tal’udu

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da aza harsashin aikin gadojin sama da za’ayi su a shatale-talen Tal’udu da Ɗan Agundi a yau juma’a da za’a kashe akalla Naira Biliyan 27.

Da yake karin bayani gwamnan jihar ta Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kuma ce, aikin za’ayi shi ne domin samarwa al’umma sauki a fannin zirga-zirga, bisa yadda ake samun yawaitar cinkoso a guraren.

“Wannan aikin za’ayi shi ne haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomin jihar mu domin aikin al’umma, “in ji Abba Gida-gida”.

A yayin ƙaddamar da aza harsashin aikin gadojin biyu dai gwamnan ya samu rakiyar mataimakin sa Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, da tsohon mataimakin gwamnan jihar ta Kano Farfesa Hafiz Abubakar da sauran Kwamishinoni, da kuma sauran mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *