May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ƴan bindiga sun sake kai hari Filato

1 min read

An kashe mutum biyu a wani hari da ƴan bindiga suka kai kauyen Durbi da ke gundumar Shere a karamar hukumar Jos ta Gabas.

Harin dai na zuwa ne a daidai lokacin da jihar ke cikin alhinin wani hari da ƴan bindiga suka kai a jajiberin Kirsimeti da ya hallaka mutum fiye da 140 a kananan hukumomin Bokkos da Barkin-Ladi na jihar.

Gidan talabijin na Channels ya ambato Shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Markus Nyam cewa maharan sun mamaye kauyen ne a daren Asabar inda suka kashe wani uba da ɗansa.

Nyam ya kuma ce ƴan banga sun yi artabu da maharan inda suka samu nasarar kashe ɗaya daga cikinsu yayin da wasu suka gudu.

Haka-zalika dakarun Operation Safe Haven sun kai ɗauki nan take, tare da hana maharan ƙara yin ɓarna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *