May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hisba ta kama babbar mota maƙare da dubban kwalaben giya a Kano

1 min read

Hukumar hisba a jihar Kano ta ce ta kama wata babbar mota maƙare da kwalaben barasa sama da 24,000.

Daraktan gudanarwar hukumar, Alhaji Abba Sufi ne ya bayyana haka ranar Laraba lokacin da yake duba motar da jami’ansa suka kama cikin dare a kan titin zuwa Zaria.

Mallam Abba Sufi ya ce jami’an Hisba suna aiki tuƙuru wajen yaƙar masu safarar miyagun ƙwayoyi da barasa zuwa jihar ta iyakokin ƙasashe maƙwabta.

Ya kuma yaba wa jami’an hukumar kan yadda suke haɗa kai da masu ruwa da tsaki wajen yakar masu safarar giya a Kano bisa tsarin shari’a.

A nasa jawabin, wani jami’in hukumar Fu’ad Ɗorayi ya ce an kama matuƙin babbar motar da ƙarin mutum biyu.

Hukumar Hizbah ta Kano ta saba kamawa da fasa kwalaben giya a jihar, saboda a cewarta yin hakan ya safara da shan barasa sun saɓa wa koyarwar Musulunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *