May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kano zatayi asarar Wutar Lantarki Mai karfin Mega Watt 2,000 Idan Bata Dauki Matakin Gaggawa ba

1 min read

Akwai Muhimmin aikin samarwa Jihar Kano Wutar wadda Gwamnatin Tarayya da Bankin duniya suke Gudunawarwa a Jihar ta Kano Amma yana Neman Subucewa.

Hakan ya biyo Bayan Gaza Samar da filaye ga wadanda aikin ya biyo ta gidajensu a yankin da ake Gudanar da aikin Samar da wutar

Acewar Engr Rabiu Haruna Wanda Kuma shine Shugaban Kungiyar Kwararru ta Jihar Kano yace sun Bayar da shawarwari a rubuce da Kuka baka da baka ga Gwamnatin Jihar Kano Dan Haka ya Bukaci Daukar Matakin Gaggawa akai

Engr Rabiu Haruna ya Kara da Cewa sakamakon samun sauyin Sabuwar Gwamnatin Tarayya za a iya dauke manyan na’ourorin da aka Samar tare da karkatar dasu Wani bangare na Kasar Nan

Idan aka kammala aikin Zai Samar da Wutar da zata baiwa Jihar Kano da Katsina da Yobe Harma da Wani bangare na jamhuriyyar Niger.

Mikiya Hausa Times ta rawaito Cewa aikin yanzu haka ya Kai kaso 90% cikin Dari Kuma akwai Muhimman kayayyaki da za ‘iya kwashesu idan Gwamnatin Jihar Kano Bata mayar da hankali akai ba.

Akarshe Engr Rabiu Haruna ya Kara kira da Babbar murya ga Gwamnan Jihar Kano Engr Abba Kabir Yusuf da duk wadanda ke da alhaki akan Gudanar da aikin da suyi Abinda ya Dace Domin kaucewa asararsa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *