May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kano pillars zata biya tarar Naira miliyan 10 sakamakon laifukan da magoya bayan Kungiyar Suka aikata

1 min read

Hukumar NPFL taci tarar Kano Pillars Naira Miliyan 10, saboda Tsaikon da magoya baya suka haifar yayin da ake kai tsaka da kawo wasan ƙungiyar da Plateau United a ranar Lahadin da ta gabata.

Sannan Kano Pillars zata biya tarar Naira Miliyan 1 sakamakon magoya bayan ta sun aikata laifin jefa abubuwa cikin filin wasa. Bugu da ƙari ƙungiyar zata bada Naira Miliyan 1 sakamakon karya dokar da sukayi na kawo tsaiko a wasan.

Ƙungiyar zata biya Tarar Naira 250,000 Diyya ga mataimakin Alƙalin wasa Sodiq Adejumo sakamakon raunin da akaji masa.

Haka zalika ƙungiyar zata buga wasanta na gaba a Gida ba tare da magoya baya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *