May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotun Koli ta Yanke Hukunci Kan Shari’ar Zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa wanda hakan ya kawo karshe lamarin

2 min read

A ranar Laraba ne kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar SDP, Dr Umar Ardo, ya shigar kan zaben gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

Ardo ya garzaya kotun kolin ne yana neman a yi watsi da hukuncin kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Adamawa da kotun daukaka kara da ke Abuja wanda a baya ya tabbatar da nasarar zaben Fintiri.

A lokacin da aka kira Shari’ar a ranar Laraba, lauyan Ardo, Mista Sylvester Imahnobe, yayin da yake amsa tambayoyi daga kwamitin mutane biyar na alkalai karkashin jagorancin mai shari’a John Inyang Okoro, ya shaida wa kotun kolin cewa wanda yake karewa da ya samu kuri’u sama da 6,000 a zaben da ya gabata shi ne yayi nasara.

Wanda ya shigar da kara ya bukaci kotun ta soke zaben da ya samar da Fintiri a matsayin gwamnan jihar Adamawa saboda rashin bin dokar zabe.
Wani mamba a kwamitin mai shari’a Emmanuel Agim ya tambayi lauyan yadda rashin bin ka’ida ya shafi sakamakon zaben ko kuma sahihancin zaben, amma lauyan ya kasa tabbatar da yadda rashin bin ka’ida ya shafi sakamakon zaben gwamnan na jihar Adamawa.

A nasa bangaren, Mai shari’a Okoro, ya shaida wa lauyan cewa tambayar da Justice Again ya yi masa, da kuma amsar da ya bayar hakan ya nuna cewa karar ba ta da inganci.

Don haka, Mai shari’a Okoro ya yi watsi da karar, sannan ya tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta Yanke akan Shari’ar.

Kotun daukaka kara, a hukuncin da mai shari’a Ugochukwu Ogaku ya yanke, ta amince da kotun cewa wadanda suka shigar da karar ba su tabbatar da zargin almundahana da rashin bin dokar zabe da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *