May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

An sace mutane 63 cikin kwanaka 18 a Abuja – Masana

1 min read

Masana harkokin tsaro da tattara bayanai sun ce an sace mutum 63 a birnin tarayyar Abuja daga ranar 1 gawatan Janairu zuwa 18 ga watan.

Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting ne ya bayyana haka a shirin Ra’ayi riga na BBC Hausa wanda ya gudana a jiya Juma’a.

Ya ce harkokin tsaro a babban birnin Abuja na ƙara taɓarɓarewa, ta yadda kusan kullum sai an samu rahoton sacewa ko kuma yunƙurin sace wani mazaunin birnin.

Barista Bulama Bukarti wanda ya kasance cikin shirin a nasa ɓangaren ya ce a matsayin Abuja na fuskar Najeriya, garin na fuskantar gagarumar barazana.

Ya ce “baya ga sace-sacen mutane da ake yi, akwai matsalar fashi da makami da kuma yi wa mata fyaɗe”.

Kuma acewarsa idan aka bari wannan lamari ya ci gaba sai ya kori kusan dukkan masu zuba hannayen jari na ƙasashen ƙetare.

Wannan matsala dai ta fi haikewa ƙananan ma’aikatan gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *