May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hukumar Kula da Zirga zirgar Ababen Hawa ta jiha KAROTA ta karyata wani rubutu da ta gani yana yawo akan ayyukan Hukumar

1 min read

Shugaban Hukumar KAROTA Engr Faisal Mahmud Kabir ne ya karyata hakan, bayan da aka kula da rubutun yana yawo a Soshiyar Midiya wanda aka yi masa suna da “SABABBIN DOKOKIN HUKUMAR KAROTA”

Hukumar ta ce wannan rubutu da ke kunshe a cikin Soshiyar Midiya baya cikin Sabbin Dokokin da aka sabunta a shekara ta 2022 na kundin dokar da ta kafa KAROTA a shekara ta 2012.

Hukumar ta ce za ta ci gaba da kama tare da gurfanar da wadanda suke yada rubuce-rubucen karya da sunan Hukumar wajen jami’an Yansanda

Tuni Hukumar tare da jami’an tsaro suka dukufa wajen nemo waðanda suke yada jita-jitar tare da gurfanar da su a gaban sharia

A karshe Hukumar ta ce ta kusa kammala shirinta na fassara sabuwar Dokar Hukumar da aka sabunta a shekara ta 2022 wadda za a fassarata zuwa harshen Hausa domin saukakawa jama’a fahimtar abinda ke kunshe a cikin sabuwar dokar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *