May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Ya kamata Gwamnati da sauran Hukumomin a Nigeria da su dauki mataki kan tsadar kayan masarufi – Dr Aliyu Dahiru

3 min read

Yanayin Rayuwa da Ake Ciki: Shiriya daga Al-Qurani
Bismillahirrahmanirrahim
Babu shakka aluma ana cikin wani hali mai wahalar gaske, babu babba babu yaro, babu mace babu namiji, babu maikudi babu talaka duka an shiga rudani illa kalilan. A yanayin da ake ciki wasu ma sun fara debe tsammani akan gyaruwar alamura saboda kullum gara jiya da yau.

Lissafi ya kufcewa mtane da yawa illa kalilan. Wata kila mai karatu ya na san ya ji inda mafitar take cikin sauri toa abiyo mu a hankali.

To gaskiya bayan na fara wani dogon rubutu sai na yanke shawarar kawai na kawo jerin Gwanon Ayoyin da suka zo a cikin sura kwaya daya tak wato Suratu Baqara domin haskakawa ga inda mafitar ta ke.

Suma iya fahimtata ce kuma a gaban su da bayansu duka akwai makamansu da za a iya karawa. Wannan ba tafsiri ba ne, sai dai maanoni bisa tafsirin maluma da na karanta na yi sharhi.

Mabudi na wadannan ayoyi suna ayoyi guda 3 na farkon surar wanda Allah Tabaraka wa Taala Yayi nuni ga cewa shidai wannan littafin shiriya ne kawai binsa zaayi ba tiyori ba ne amma kadai ga wadanda suka yadda da gaibu kuma sukayi aikin kwarai.

الٓمٓ (١) ذَٲلِكَ ٱلۡڪِتَـٰبُ لَا رَيۡبَ‌ۛ فِيهِ‌ۛ هُدً۬ى لِّلۡمُتَّقِينَ (٢) ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَـٰهُمۡ يُنفِقُونَ (٣
Sai na shallaka na tafi zuwa aya ta 152 zuwa ta 157 inda Allah yayi shela akan a tuna da shi zai tuna da ku kuma yayi kira da a nemi dauki daga sallah da hakuri domin yana tare da masu hakuri.

Mai Hikima Jalla wa Aala sai yace to zai jarrabi mutane da wani abu na tsoro da yunwa da tauyaya ta dukiya da rayuka da amfanin gona, Amma masu hakuri ayi musu bishara sune wadanda suke komawa ga Allah a ko wane hali.

Wannan yayi daidai da halin da muke ciki.
فَٱذۡكُرُونِىٓ أَذۡكُرۡكُمۡ وَٱشۡڪُرُواْ لِى وَلَا تَكۡفُرُونِ (١٥٢) يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ ٱسۡتَعِينُواْ بِٱلصَّبۡرِ وَٱلصَّلَوٰةِ‌ۚ إِنَّ ٱللَّهَ مَعَ ٱلصَّـٰبِرِينَ (١٥٣) وَلَا تَقُولُواْ لِمَن يُقۡتَلُ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ أَمۡوَٲتُۢ‌ۚ بَلۡ أَحۡيَآءٌ۬ وَلَـٰكِن لَّا تَشۡعُرُونَ (١٥٤) وَلَنَبۡلُوَنَّكُم بِشَىۡءٍ۬ مِّنَ ٱلۡخَوۡفِ وَٱلۡجُوعِ وَنَقۡصٍ۬ مِّنَ ٱلۡأَمۡوَٲلِ وَٱلۡأَنفُسِ وَٱلثَّمَرَٲتِ‌ۗ وَبَشِّرِ ٱلصَّـٰبِرِينَ (١٥٥) ٱلَّذِينَ إِذَآ أَصَـٰبَتۡهُم مُّصِيبَةٌ۬ قَالُوٓاْ إِنَّا لِلَّهِ وَإِنَّآ إِلَيۡهِ رَٲجِعُونَ (١٥٦) أُوْلَـٰٓٮِٕكَ عَلَيۡہِمۡ صَلَوَٲتٌ۬ مِّن رَّبِّهِمۡ وَرَحۡمَةٌ۬‌ۖ وَأُوْلَـٰٓٮِٕكَ هُمُ ٱلۡمُهۡتَدُونَ (١٥٧) ۞
A wasu ayoyin sai Mahlicci ya nuna ba kallon gabas ne tsoron sa kadai ba aa akwai sauran abubuwa kamar ciyar da dukiya a lokacin da kake tsananin santa kamar yanayin mu da ake ciki ga na kusa da mabukata har yan tafarki.

Bayan haka sai cika alkawari da hakuri a kowane hali. Hakana tsayar da haddi domin tanan ne kadai za ka bawa kowa garanti na rayuwa wani ba zai kashe wani ba a banza kuma ya wuce, to an sanya cewa rayuwar aminci tana cikin yin kisasi.
لَّيۡسَ ٱلۡبِرَّ أَن تُوَلُّواْ وُجُوهَكُمۡ قِبَلَ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَلَـٰكِنَّ ٱلۡبِرَّ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأَخِرِ وَٱلۡمَلَـٰٓٮِٕڪَةِ وَٱلۡكِتَـٰبِ وَٱلنَّبِيِّـۧنَ وَءَاتَى ٱلۡمَالَ عَلَىٰ حُبِّهِۦ ذَوِى ٱلۡقُرۡبَىٰ وَٱلۡيَتَـٰمَىٰ وَٱلۡمَسَـٰكِينَ وَٱبۡنَ ٱلسَّبِيلِ وَٱلسَّآٮِٕلِينَ وَفِى ٱلرِّقَابِ وَأَقَامَ ٱلصَّلَوٰةَ وَءَاتَى ٱلزَّڪَوٰةَ وَٱلۡمُوفُونَ بِعَهۡدِهِمۡ إِذَا عَـٰهَدُواْ‌ۖ وَٱلصَّـٰبِرِينَ فِى ٱلۡبَأۡسَآءِ وَٱلضَّرَّآءِ وَحِينَ ٱلۡبَأۡسِ‌ۗ أُوْلَـٰٓٮِٕكَ ٱلَّذِينَ صَدَقُواْ‌ۖ وَأُوْلَـٰٓٮِٕكَ هُمُ ٱلۡمُتَّقُونَ (١٧٧) يَـٰٓأَيُّہَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ كُتِبَ عَلَيۡكُمُ ٱلۡقِصَاصُ فِى ٱلۡقَتۡلَى‌ۖ ٱلۡحُرُّ بِٱلۡحُرِّ وَٱلۡعَبۡدُ بِٱلۡعَبۡدِ وَٱلۡأُنثَىٰ بِٱلۡأُنثَىٰ‌ۚ فَمَنۡ عُفِىَ لَهُ ۥ مِنۡ أَخِيهِ شَىۡءٌ۬ فَٱتِّبَاعُۢ بِٱلۡمَعۡرُوفِ وَأَدَآءٌ إِلَيۡهِ بِإِحۡسَـٰنٍ۬‌ۗ ذَٲلِكَ تَخۡفِيفٌ۬ مِّن رَّبِّكُمۡ وَرَحۡمَةٌ۬‌ۗ فَمَنِ ٱعۡتَدَىٰ بَعۡدَ ذَٲلِكَ فَلَهُ ۥ عَذَابٌ أَلِيمٌ۬ (١٧٨) وَلَكُمۡ فِى ٱلۡقِصَاصِ حَيَوٰةٌ۬ يَـٰٓأُوْلِى ٱلۡأَلۡبَـٰبِ لَعَلَّڪُمۡ تَتَّقُونَ (١٧٩)

Abin shaawar kuma sai a aka shiga batun cin dukiya bisa tsarin da Allah ya yarda da shi banda haram ko zalinci. Anan na barku kowa ya kawo misalign da ya fi sani.
وَلَا تَأۡكُلُوٓاْ أَمۡوَٲلَكُم بَيۡنَكُم بِٱلۡبَـٰطِلِ وَتُدۡلُواْ بِهَآ إِلَى ٱلۡحُڪَّامِ لِتَأۡڪُلُواْ فَرِيقً۬ا مِّنۡ أَمۡوَٲلِ ٱلنَّاسِ بِٱلۡإِثۡمِ وَأَنتُمۡ تَعۡلَمُونَ (١٨٨) ۞
Hakana Ubangiji Mai Girma da Daukaka ya shelanta cewa idan suka tambaye ka Ya Annabi Muhammad s.a.w game da ni ka gaya musu ina kusa, kawai su roke ni zan amsa musu. Allahu Akbar! Ko zalimci ne, ko bukatace, ko ibtilai ne kofa a bude ta ke.

وَإِذَا سَأَلَكَ عِبَادِى عَنِّى فَإِنِّى قَرِيبٌ‌ۖ أُجِيبُ دَعۡوَةَ ٱلدَّاعِ إِذَا دَعَانِ‌ۖ فَلۡيَسۡتَجِيبُواْ لِى وَلۡيُؤۡمِنُواْ بِى لَعَلَّهُمۡ يَرۡشُدُونَ (١٨٦)
Haka na aka kara dawowa kan batun dukiya cewa ku ciyar da dukiya ka da ku jefa kan ku izuwa halaka. Ashe rashin ciyarwa halaka ya ke kai mutane.

وَأَنفِقُواْ فِى سَبِيلِ ٱللَّهِ وَلَا تُلۡقُواْ بِأَيۡدِيكُمۡ إِلَى ٱلتَّہۡلُكَةِ‌ۛ وَأَحۡسِنُوٓاْ‌ۛ إِنَّ ٱللَّهَ يُحِبُّ ٱلۡمُحۡسِنِينَ (١٩٥)
Wasu ayoyin kuma suka sifanta mutanen da suke nuna su na Allah ne amma da sun juya baya sunfi kowa barna wajan barnatar da dabbobi, kayan abinci da gallazawa mutane.

وَمِنَ ٱلنَّاسِ مَن يُعۡجِبُكَ قَوۡلُهُ ۥ فِى ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا وَيُشۡهِدُ ٱللَّهَ عَلَىٰ مَا فِى قَلۡبِهِۦ وَهُوَ أَلَدُّ ٱلۡخِصَامِ (٢٠٤) وَإِذَا تَوَلَّىٰ سَعَىٰ فِى ٱلۡأَرۡضِ لِيُفۡسِدَ فِيهَا وَيُهۡلِكَ ٱلۡحَرۡثَ وَٱلنَّسۡلَ‌ۗ وَٱللَّهُ لَا يُحِبُّ ٱلۡفَسَادَ (٢٠٥)
Duk da haka wasu ayoyin suna tunatar da mu taimakekeniya da cudanni in cude ka wadda itace take kawo zaman lafiya da maslaha sabanin barna irin wadda wasu ke aikatawa.

وَلَوۡلَا دَفۡعُ ٱللَّهِ ٱلنَّاسَ بَعۡضَهُم بِبَعۡضٍ۬ لَّفَسَدَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَلَـٰڪِنَّ ٱللَّهَ ذُو فَضۡلٍ عَلَى ٱلۡعَـٰلَمِينَ (٢٥١) تِلۡكَ ءَايَـٰتُ ٱللَّهِ نَتۡلُوهَا عَلَيۡكَ بِٱلۡحَقِّ‌ۚ وَإِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ (٢٥٢) ۞
Ubangiji Mai Girma da Daukaka ya kara da cewa ku ciyar da dukiya kafin ranar da babu ciniki ko wata MOU ta kasuwanci da makamantan su.

يَـٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَنفِقُواْ مِمَّا رَزَقۡنَـٰكُم مِّن قَبۡلِ أَن يَأۡتِىَ يَوۡمٌ۬ لَّا بَيۡعٌ۬ فِيهِ وَلَا خُلَّةٌ۬ وَلَا شَفَـٰعَةٌ۬‌ۗ وَٱلۡكَـٰفِرُونَ هُمُ ٱلظَّـٰلِمُونَ (٢٥٤)
Abin shaawar shine duka kwarafniya da zaa shiga Allah yayi Alkawarin tsare bayinsa ta hanyar haskaka musu tare da fitar da su daga duhu zuwa haske sabanin wadanda suka bata da dagutu ke diban su daga haske zuwa duhu.

ٱللَّهُ وَلِىُّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يُخۡرِجُهُم مِّنَ ٱلظُّلُمَـٰتِ إِلَى ٱلنُّورِ‌ۖ وَٱلَّذِينَ كَفَرُوٓاْ أَوۡلِيَآؤُهُمُ ٱلطَّـٰغُوتُ يُخۡرِجُونَهُم مِّنَ ٱلنُّورِ إِلَى ٱلظُّلُمَـٰتِ‌ۗ أُوْلَـٰٓٮِٕكَ أَصۡحَـٰبُ ٱلنَّارِ‌ۖ هُمۡ فِيہَا خَـٰلِدُونَ (٢٥٧)
Ya Allah Ka zama Mai Jibintar al`amuran mu Ka fitar da mu daga duhu zuwa haske Ya Allah.
Aliyu Dahiru Muhammad
20 Rajab 1445. (1/2/2024)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *