May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Rundunar ‘Yan Sandan Kano ta Sanya dokar takaita zirga- zirga a gobe Asabar

2 min read

Rundunar yan sandan jahar Kano, tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun shirya tsaf domin bayar da cikakken tsaro a kananan hukumomin da za a sake gudanar da zabukan yan majalissun dokokin jahar, a ranar Asabar 3 ga watan Fabarairun 2024.

Kwamishinan yan sandan jahar Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce, zaben zai shafi kananan hukumomi shida rumfunan zabe 66 a mazabun yan majalissu uku da suka hada da Tsanyawa/Kunchi, Kura/Garun Mallam da kuma Tofa/Rimin Gado

CP Gumel, ya kara da cewa rundunar ta takaita zirga-zirga a kananan hukumomin da zaben ya shafa, in banda masu gudanar da aiyuka na musamman kamar motocin Ambulance, kwana-kwana, jami’an lafiya da kuma manema labarai da hukumar zaben ta tantance su.

Haka zalika rundunar ta hana jami’an ta yin rakiyar masu rike da mukaman siyasa a dukkanin rumfunan zaben.

Kwamishinan yan sandan jahar CP Muhammed Usaini Gumel, gargadi yan daba da kuma yan siyasar dake yunkurin shigo da yan dabar daga wasu wurare da cewar an tanadi jami’an tsaro isassu domin cafke dukkan wanda yake yunkurin tayar da hartsigi.

Rundunar ta haramta daukar dukkan wani makami tare da cewa masu son haifar da ya mutsi su kuka da kansu domin rundunar ba za ta zura mu sui do ba.

Sai dai sanarwar ta ce iya wadanda hukumar zaben ta tantance ne kawai za a bari su kada kuri’arsu kuma wadanda katin zaben su ya yi daidai da wajen da aka tantance su

Rundunar ta ce ba a yarda hukumomin da bana gwamnatin tarayya ba , suje wajen domin bayar da tsaro da suka hada da Hisbah, Karota, Bigilanti,Man Over, Boys Scourt daidai ba a amince suje wajen zaben ba.

Haka zalika rundunar ta yi kira ga al’ummar jahar Kano su bayar da hadin kai domin gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali.

Ga nambobin karta kwana 08032419754, 08123821575, 09029292926, ko NPF Rescue Me @ Play Store or through the

Shafukan sada zumunta

*Facebook: Kano State Police Command*
*Twitter: Kano State Police Command*
*Instagram: Kano State Police Command*
*Tiktok: Kano State Police Command.*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *