May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Da alama Amurka ta sayar wa Najeriya manyan makamai domin wata manufa

3 min read

Gwamnatin Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya wasu manyan makamai domin yaki da yan bindiga da kuma mayakan Boko Haram a sassan kasar.

An fara wannan ciniki ne tun shekarar 2022, amma ya gamu da jinkiri sakamakon matakin da wasu yan majalisar dokokin Amurkar suka dauka, na dakatar da cinikin har sai Najeriya ta cika wasu sharudda, domin tabbatar da cewa makaman ba su yi wata illa ga farar hula ba.

Ko da yake, Najeriya ta bayar da kwangiloli da dama na sayen makamai, amma wannan ita ce mafi girma a tarihin hada-hadar makamai tsakanin Najeriya da Amurka, domin hatta jiragen Tucanon da Najeriya ta saya a baya bayan nan ma, dala miliyan 600 aka kashe wajen sayansu, kasa da dala biliyan guda da ake magana a yanzu.

Jirage ne samfurin 12 AH 1Z, da kuma wasu kwamfutocin tsaro masu gani har hanji, da za su ba da damar tattara bayanan sirri, da kuma taimakawa jiragen wajen kai hare-hare.

Group Captain Sadiq Garba Mai rtaya, masanin tsaro ne a Njeriya, wanda ke bibiyar yadda cinikin makaman ke kasancewa tun 2022.

Ya ce ‘‘Jirgi ne wanda an yi amfani da shi tun lokacin yakin Vietnam, ana amfani da shi ne a raka sojoji a kasa, kamar shi yana sama yana share fage ga sojojin da ke kasa a yayin kai farmaki, abin da ake kira ‘Close Air Support’. Ya na dauke da bindiga mai baki guda uku, wadda za ta iya harbi mai tsawon kilomita 2, tana kuma dauke da harsashi har 750. Jirgin kuma ya na iya daukar makami mai linzami, gashi kuma zai iya aiki da dare’’

Masanin ya kara da cewa baya ga wadannan jirage, akwai kuma wasu kwamfutoci da ke cikin wannan hada-hada da za su tamaka wajen ganin an kiyaye fararen hula, wani abu da zai taimaka don ganin ba a maimaita irin abubuwan da suka faru a baya ba.

‘‘Suna sa mai tukin jirgin ya kara tabbatarwa da abin da yake gani, jirgin yana da na’urorin da ke tantance wadanda za a kai wa hari; shin mutanen gari ne ko abokan gaba. Abin da ake sa rai, da irin wannan jirgi ba za a samu hatsari irin wanda aka samu a Tudun Biri ba’’

A baya dai, Amurka na takatsantsan wajen sayarwa Najeriya makamai saboda zargin suna rutsawa da fararen hula,shi yasa ma a wannan karon sai da aka yi yarjejeniyar biyan kudin ba da horo wamfani da su, don haka a cewar Group Captain Sadiq Garba Mai Ritaya, sai an yi takatsantsan don ganin ba a sake mayar da hannun agogo baya ba.

A cewar sanarwar ma’aikatar harkokin wajrn Amurkar wadannan makaman za su kara wa Najeriya karfin kai hare-hare da kuma mayar da martani cikin gaggawa domin tsaro da zaman lafiyar kasar baki daya.

Matsalolin tsaro masu sarkakiya a Najeriya sun raba miliyoyin mutane da muhallansu tare da salwantar rayuka da dama, sai dai ana sa ran wadannan makamai da za a kamala hada hadar su zuwan watan Yunin wannan shekara, za su taimaka wajen yakar matsalar.

Ba dai wannan ne karon farko ba da Najeriya ke sayen makamai irin wadannan, said ai abun jira a gani a yanzu shine ko za su taka rawar da ake tsamani ko kuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *