May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Mazauna birnin Minna na gudanar da zanga-zangar game da tsadar rayuwa

1 min read

Al’umma a Minna, babban birnin jihar Neja na gudanar da zanga-zanga kan tsadar rayuwa a Najeriya inda suka rufe manyan titunan da ke birnin.

Masu zanga-zangar sun hada da mata da matasa inda suke rera wakoki yayin da jami’an tsaro har da yan sanda ke gefe suna kallo.

Wasu mazauna birnin da suka tattauna da BBC sun ce tsadar kayan masarufi da rashin tabuka abin a zo a gani daga bangaren gwamnati wajen samar da sauki a lamarin ne ya tilasta musu rufe manyan tituna domin gwamnati ta ji kukansu.

Mataimakin gwamnan jihar Neja, Yakubu Garba a lokacin da yake yi wa masu zanga-zangar jawabi, ya ce gwamnati tana sane da irin kunci da wahalar da jama’a suke fuskanta a yanzu.

Ya ce gwamnati tana aiki domin rage halin matsi da aka shiga da kuma tasirin da ake gani sanadin cire tallafin mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *