May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

’Yan Bindiga Na Neman 40m Kudin Fansar Matar Basaraken Kwara

1 min read

Yan bindigar da suka kashe wani basarake tare da sace matarsa, sun rage kudin fansar da suke nema daga Naira miliyan 100 zuwa Naira miliyan 40 a Jihar Kwara.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa a maharan sun tuntubi iyalan basaraken kan a biyan su Naira miliyan 100 kudin fansar matar.

Maharan sun kashe basaraken fadar Olukoro na yankin Koro-Ekiti, Oba Olusegun Aremu-Cole, a Karamar Hukumar Ekiti ta Jihar a daren ranar Alhamis.

Bayan kashe basaraken, maharan sun yi awon gaba da matarsa da wani mutum daya.

Tuni rundunar ’yan sandan jihar ta aike dakaru yankin don tabbatar da tsaro tare da yin bincike kan kisan basaraken.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *