May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Idan kasan ka boye kayan abinci ka fito dashi kafin muzo – Hukumar karbar korafe -korafe Kano

1 min read

Shugaban hukumar karbar korafe korafe da yaki da cin hanci da Rashawa ta jihar Kano Barrista Muhyi Magaji Rimin Gado zai fara Kai ziyara runbunan ajiyar Kayan Abinci a Kano Dan fito da abincin da aka boye a sayarwa da jama’a.

Barista Muhyi Magaji Rimin Gado yace Haramun ne Kuma karya dokar kasa ne boye abinci Lokacin da ake tsanananin wahalar abinci a kasa .

Za’a fara Kai samamen guraren da ake zargi an boye kayan Abinci ne kafin watan Azumin Ramadan.

Muhyi Magaji Rimin Gado yace wajen da zasu fara Dira shine Kasuwar Dawanau inda yace duk Wanda aka kama ya boye abinci za’a fito da abincin a kaishi kasuwa, wanda hakan Zai taimaka wajen sauko da farashin kayan Abinci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *