May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotu ta umarci gwamnatin Najeriya ta tsayar da farashin kayayaki cikin kwana bakwai

1 min read

Wata kotun tarayya da ke Legas a Najeriya ta umarci gwamnatin kasar da ta gaggauta tsayar da farashin kayayakin harkokin yau da kullum da man fetur da dangoginsa a daukacin fadin kasar cikin kwanaki bakwai.

Mai shari’a Ambrose Lewis-Allagoa ne ya bayar da umarnn inda ya bukaci gwamantin ta tsayar da farashin madara, da fulawa, da sukari, da keke, da kayan gyaransa.

Sauran sun hada da, ashana, da babur da kayan gyaransa, da motoci da kayan gyaransu, da man fetur, da kanazir, da gas din girki, da kuma diseal.

Mai shari’a Lewis-Allagoa ya bayar da wannan umarnin ne a lokacin da ya ke bayar da hukucin kan karar da lauyan nan mai rajin kare hakkin dan adam Femi Falana ya shigar, yanan karar hukumar Kayyade Farashin kayayaki, da minsitan shari’a na kasar.

Falana ya garzaya gaban kotun tarayyar ne ya na neman ta yi masa fashin baki kan sashe na 4 na dokar da ta kafa hukumar Kayyade Farashi, wadda aka dorawa alhakin tsayar da farashi kowane irin kaya a Najeriya, kamar yadda yake a kundin dokar kayyade farashin kayyayaki na Najeriyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *