May 20, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Za’a mayar da wasu ofisoshin NUPRC zuwa Lagos

2 min read

Hukumar NUPRC mai sa ido kan harkokin man fetur a cikin ruwa a Najeriya ta kammala shirye-shiryen sauya matsugunnin wasu ofisoshinta daga Abuja zuwa Legas.

Wannan da alama na zuwa ne bayan matakin baya-bayan nan na mayar da wasu ma’aikatan babban bankin Najeriya, CBN da sauya matsugunin hukumar kula da tashoshin jiragen sama ta Najeriya – FAAN da wani sashe na babban bankin kasar, CBN.

Wasu ma’aikatan NUPRC sun tabbatar wa BBC cewa hukumar na shirye-shiryen ɗaukan wannan matakin.

Matakin na mayar da wasu ma’aikatan CBN zuwa Legas da ɗauke hukumar FAAN zuwa BIRNIN ya janyo cece-kuce inda masu ruwa da tsaki suka nuna rashin gamsuwarsu da matakin.

NUPRC da a baya ake kira DPR mai sa ido kan harkokin haƙowa da sayar da man fetur a Najeriya, sashe ne a ƙarƙashin ma’aikatar albarkatun man fetur ta Najeriya.

Hukumar na lura da mai da iskar gas domin tabbatar da bin ƙa’idoji da dokokin da suka dace da kuma lura da wasu dokoki da suka shafi fita da shigowa da albarkatun mai cikin Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban hukumar, Gbenga Komolafe ya soma yunƙurin sauya matsugunin wasu ofishoshin hukumar daga Abuja.

To sai dai wani babban ma’aikaci a hukumar wanda ya zanta da BBC, ya musanta kalaman na shugaban hukumar.

“Ya yi iƙirarin rashin isasshen wuri ga sabbin ma’aikatan da yake son ya ɗauka aiki. Wannan ba dalili ba ne kasancewar shekaru biyu da suka gabata ne aka ɗauke ofishin daga Legas zuwa Abuja, sannan ana gab da ƙarasa makeken ginin hedikwata.” In ji ma’aikacin.

Sabuwar hedikwatar gini ne mai hawa 10 da majalisar zartarwa ta gwamnatin tarayya ta amince da shi a 2020 wanda kuma aka tsara kammalawa cikin wata ashirin da huɗu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *