May 21, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Hauhawar farashi a Najeriya na neman wuce tunanin mutane

1 min read
Hauhawar farashi a Najeriya na neman wuce tunanin mutane

Najeriya, masana na ganin cewa matukar ba ƙwararan matakan da suka kamata aka bi ba, to da wuya a magance matsalar ta hauhawar farashin kaya da ta tsadar rayuwa a kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan ƙasar ke ci gaba da kokawa game da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar rayuwa.

Hukumomi dai na ta bayar da tabbacin cewa suna bin matakan da suka dace domin shawo kan lamarin.

Farfesa Kabiru Isa Dandago, wani masani a fannin ƙididdigar kuɗi da tattalin arziki a jami’ar Bayero ta Kano, yana ganin cewa da wuya a iya daƙile hauhawar farashin kayyaki a Najeriya cikin ƙaramin lokaci.

Masanin ya yi gargaɗin cewa matuƙar ba a hankali ba wannan lamari ba zai zama alkairi ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *