May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Gwamnatin Kano ta magantu kan zarginta da sakin Murja Ibrahim

1 min read

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan ma’aikatar yaɗa labarai ta jihar Kano, Bala Halilu Dantiye, inda yace gwamnatin jihar na sane da tanadin da kundin tsarin mulkin kasar nan yayi na raba iko ga wanne bangare na mulkin dimokaradiyya, wadanda suka hadar da bangaren shari’a, majalisa da kuma na zartaswa.

Sanarwar tace ana kira ga jama’a da su yi watsi da zargin da ake yi wa gwamnatin jihar, wanda wasu ke kokarin bata mata suna tare da tabbatar wa al’ummar jihar cewa za ta ci gaba da mutuntawa tare da kiyaye alfarmar dokoki da kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *