May 27, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke wa Yar TikTok Ramlat Muhammad Hukuncin zama a gidan Gyaran Hali

1 min read

Kotun shari’ar Muslunci da ke Hisbah a jihar Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Sani Tanimu Hausawa, ta yanke hukuncin dauri a gidan yari na wata bakwai da zaɓin tarar N50,000 ga matashiyar ’yar TikTok, Ramlat Muhammad.

Tunda fari Hisbah ta gurfanar da matashiyar ne bisa tuhume-tuhumen fitsara da rashin tarbiyya da yada ɓaɗala, yawon banza da ta zubar sai kuma fitsara wanda ya saba da sashe na 385.

A tuhumar farko alkalin ya yanke wa Ramlat hukuncin zaman gidan yari na tsawon wata uku ko zabin tara ta Naira dubu talatin.

Sai laifin yawon banza, wanda a kansa alkalin ya yanke mata hukuncin daurin wata uku a ko zabin tara na Naira 20,000.

A laifi na uku da aka kama ta da shi na fitsara kuma alkalin ya yanke mata hukunci bisa sassauci da ta nema zaman gidan yari na tsawon wata guda babu zabin tara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *