May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Tuni dai Kotu ta aike da Murja Ibrahim Asbiti domin bincikar Kwakwalwarta

1 min read

Kotun shari’ar muslinci ta Gama PRP karkashin jagorancin mai shari’a Nura Yusuf Ahmad, tayi umarnin a binciki lafiyar kwakwalwar ‘yar Tik-Tok din nan Murja Ibrahima kunya.

Cikin wani kwaryar kwaryar hukunci da kotun ta yi ta ayyana cewar a ajiye murja a karkashin kulawar likita kuma hukumar Hisba ta dinga lura da ita.

Mai shari’a Nura Yusuf ya bayyana cewar kasancewar ita murja ta nuna wani hali wanda yake nuna cewar kodai tana cikin maye ko kuma kwakwalwarta bata da lafiya, a dan haka ne kotun ta yi umarnin ma’aikatar lafiya ta binkici kwakwalwar ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *