May 28, 2024

Bustan Daily

Trusted Source for Online News Publishing

Wasu Al’ummar jihar Katsina sun dakawa Motar dakon Abinci na Kamfanin Dongote a jiya Litinin

1 min read

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa Al’ummar wani gari a cikin jihar sun tare motar Kamfanin Dongote dauke da kayan abinci sun daga Wawa akan kayan masarufi a yayin da motar ke kokarin tsallakawa kasar Nijar a jiya Litinin.

Wani Video dake yawo a Kafafan sada zumunta ya nuna yadda mutanan ke kwasar kayan suna zurawa a guje.

A Nigeria dai Al’umma na fama da tsadar Kayayyaki wanda ake alakanta lamarin da tsadar dalar Amurka, inda wasu kuma ke cewa cire tallafin manfetir ne ya haddasa Lamarin.

A baya -bayan ma Al’umma jihar Enugu ma sun fasa rumbun adana abinci na Gwamnati inda suka da wawa.

A Jihar Adamawa ma an Samu irin wannan labari wanda ke nuna irin bukatar Abinci Al’umma ke ciki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *